YADDA ZAKI MALLAKE SAURAYIN KI

0
 YADDA ZAKI MALLAKE SAURAYIN KI

Dayawa yan matan arewa ko nace ƙasar hausa suna da wani naƙasu a soyayya hakan yasa sauran ƙabilu sukafisu cin ribar soyayya misamman waje iya mallakar namiji.

Abun Mamaki Sai Kaga Wacce Take Yin Yare, Gata Mummuna Amma Saurayinta Duk duniya Ba Wacce Yakeso Sai Ita Saboda Yadda Yake Marari Akanta Da Sonta. Sakamakon Kulawa Da Take Bashi A Soyayya Da Ƙwarewa Wajen Iya Kalamai Da Tsari Na Soyayya,


In kunyi nazari dayawa yan matan qabilu kamar yoruba igbo, indiya, china, tu­rawa ,su a soyayya kullun burin su daɗaɗawa masoyin su suke da son suburgeshi son ya gani ya yaba, da kuma jan hankalin sa. hakan yasa suke gane meson su nahaqiqa bana sha'awa ba, sai kaga suna soyayyar su cikin kwanciyar hankali, da taimakon juna kamar wa da ƙanwa.


sabanin mu nan yan matan mu, dazarar kafara soyayya to watan baƙinciki yakama a rayuwar ka, kataro mach babba haka zaka kasance cikin damuwa yau dadi gobe baqin ciki. wai kullin kai sai dai ka rarrasheta, saidai kafaranta mata rai.





Advertisement: Buy Data Subscription at Very Chip Price  Visit:

https://www.elsub.com.ng 




1. Idan ka ƙira a waya bazata ɗauka da wuri ba.
2. Idan kaje zance taita wani nuƙu-nuƙu kan ta fito.


3. Idan tabuƙaci wani abu baka bata ba taita fushi dakai sai kace ta baka ajiya.
4. Kuyi ta faɗa akan akwati da lefe ,tana sai kayi 12 kana 6, ko kana 3 zakai tana cewa sai kayi 4, ba tausayi yadda kasan ATM Card haka suka maida namiji mafiya yawan ƴan matan hausa haka suke.

Babu abunda yafi cutar da yan matan arewa a soyayya irin RASHIN NUNA SOYAYYA GA MASOYI wai namiji akwai wulaƙanci dan haka sai anjamasa aji over. 
Bata san duk namijin da yazo wurin ki domin aure baya son jan aji ba.




AMATSAYIN KI NA BUDURWA GA YADDA ZAKI MALLAKE SAURAYINKI.

1. tashin farko kizama me kyakkyawan hali kamar gaskiya, Haƙuri, barin zargi, riƙon amana  KAMUN KAI, kunya da sauran su.



2. kizama me murmushi ga masoyinki ba me hade rai ba, ba kuma koda yaushe ba kamar kina tallan makilin.

Shi murmushi anayin sa ne yayin gai da masoyi, ko ban kwana da masoyi, ko yayin da akai wa juna satar kallo, ko yayin da aka hadu a hanya ko farkon hira, ko yayin da masoyi yafadi magana me daɗi.




YADDA ZAKIYI MURMUSHI
kidan tabe kumatunki tare da bude bakinki kamar kaso 1 cikin goma tayadda haƙoran sama yawanci masu faffadan haƙora yayin murmushi haƙora 6 ko 7 na gaba ne suke bayyana, amma masu qananan haƙora sukan zarta hakan sannan gefen dadashin sama ma in yafito kadan abun yafi armashi, sannan ana so ki dan karkatara da kanki, ko ki motsashi ko kiyi qasa da kanki kadan, yayin murmushi ana hadashi DA kallon qauna wato irin kallon da kwayar ido take komawa 55 angle na ido, ko wanda ake maida ƙwayan ido gefe irin na kallon kahadu fa.


Yar uwa murmushi nasa ki mallake saurayi sosai. SANNAN AKWAI MURMUSHI NA GANIN dama

3. nuna soyayya ga saurayinki, wato ta wadannan han yoyin
- Mai dama sa da Saƙo (Text) in yayi miki, wato reply na Saƙo domin wasu saidai kaita aikamusu saqon amma susai sun gadama zasu dawo ma dashi.


Wata sai ka taƙarƙare kayi mata kalamai masu yawa amma intatashi yimasa reply saikaga kolayi daya baikaiaba kamar bata so misali kaji tace .
- nagode nawan, ko kai nawan, ko gaskiya naji dadi, ko hmm nagode da sauran su. duk wannan ba daidai bane, yakamata yadda ya bata lokaci kema ki ƙoƙarta ki yi koda layi 3 kema ki aikamasa tabbas zai ji dadi.

- Kiran sa a lokacin da bai zataba musamman a lokacin da kike zaton yana cikin abokan sa, ko yana nishadi, a duk sadda kika kira shi yaɗau wayan sa yaga sunanki murmushi yakan farayi koda yana cikin abokan sa zai tashi da sauri in an tambayeshi me ya faru zai ce mutuniyarce yana murmushi. hakan yakan ji dadi kin kuma burgeshi kin kira shi a cikin abokansa dansusan kin damu da shi. Kuma ko zasu zugashi akan ki zasu bashi shawari ne me kyau.-

Amma da yawan ƴan mata, su sai dai kaita kiransu wata inkaga takiraka to tana buqatar wani abune ko kayi mata gorin kira, wata sai jarabar flashing kamar Jikar MTN.


- Yi masa kyauta, ta bazata komai ƙanƙantarsa musali saya masa zobe, turamasa kati koda na 10 wlh inyasan arzikin ki daidai hakan ne zai ji dadi sosai, yasan yana ranki, ko ɗan mintin nan na 30 kacal.

- Furta masa kalaman soyayya koda rabin yadda shi yake furta miki ne .

- kula da lukutan sa na zuwa Hira, neman afuwar sa in kin saba lokaci, nuna masa damuwarki in yasaba lokaci ko bai zoba har sai ya rarrasheki.

- Yawaita yimasa nasiha cikin wasa da shagwaba

- yin kwalliya yayin zuwan sa Hira, dakuma nuna masa damuwa in bai yaba kwalliyar ba.

- Nuna tausayin sa dakuma tayashi farin ciki ayayin da farinciki ya sameshi dakuma tayashi bacin rai ayayin da baƙin ciki yasameshi, da ƙoƙarin kwantar mashi da hankali.


- Girmama iyayensa .
- Nuna nishaɗi da jindadi yayin daya zo gunki.
- Kada ki tsawaita jan aji a gareshi, idan kika dan ja kadan, to zai rarrasheki, daga nan kekuma sai ki haqura,

- Kina nuna masa kina da matsayi da kima da aji ba kowani namiji yadace dake ba sai shi.

- kizama me tsari da kama mutuncinki da sanin ƴancinki a soyayya misali: ki nuna masa bacin ranki in zai saki sabon Allah koda zai dena zuwa dakan sa zai nemi gafarar ki.

- kada kizama me izza ga saurayi da nuna wa samari ke ba wani namiji da ya isa kiyi masa kaza da kaza SAMARI SUN TSANI HAKA! 

- Ki Zama Me Fuska Daya.
- Kada Kisa Girman Kai Ga Saurayin Ki,
- Kada Kuma Ki Nuna Masa Ke Marar Ƴanci Ce. Kamar In Baki Same Shi ba Mutuwa Za Kiyi A'a, Kidai Nuna Masa So Dai Dai Misali. Kada Ki boye Qaunar Da Kike Masa

Advertisement: Buy Data Subscription at Very Chip Price  Visit:

https://www.elsub.com.ng 

Tags

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)