ABUBUWAN DA SUKE BATA SOYAYYA

0
 ABUBUWAN DA SUKE BATA SOYAYYA.  

Mun san cewa ita Soyayya tana rayuwa ne akan wasu ginshiƙai, Lokacin da waɗannan ginshiƙan suka fara lalacewa, Za'a nemi shauƙi na Wannan Soyayyar a rasa.

Domin kaucewa waÉ—annan Abubuwan, mun kawo muku

wasu Abubuwa da Muke ganin suna Gaba Gana Wajen Lalata Soyayyar.

WaÉ—annan wasu halaye ne dasuke janyowa soyayya matsala ko batashi ma duka.

1. Ruwan ido 

2. Ƙarya 

3. Munafurci 

4. Son abun duniya. 

5. Zargi  


 


Advertisement: Buy Data Subscription at Very Chip Price  Visit:

https://www.elsub.com.ng 


 

1. RUWAN IDO yana da matuÆ™ar kawo matsala a soyayya, sai kaga budurwa ta tara samari samada 5 ta kasa zabar É—aya, a Æ™arshe ta zabi wanda ba nagari ba. RUWAN IDO KANSA AYIMIKIKI ZARGIN KE YAR ISKACE DAN KINA TARA SAMARI SUNAI MIKI LAYI. ZAIKUMA SA KI KIYI SAKE RESHE KAMA GANYE, DA RAGE MIKI ƘIMA KEDA IYAYENKI.  




 

2. ƘARYA. KOWA YASAN ƘARYA A SOYAYYA, IMMA SAURAYI YAYIWA BUDURWA ƘARYA DON YA MALLAKE TA, KO ITA TAYIWA SAURAYI ƘARYAR ABU kaza da kaza kamar, babban gida, mota, kudi, matsayi da sauran su alahali BABU, KO ITA TAYI MASA ƘARYAN ITA YAR WANI CE ALHALIN KUMA ƘARYA TAKE . IN ANA ƘARYA A SOYAYYA ZA A IYA FUSKANTAR WADANNAN MATSALOLIN.  

*Samari Su Tsaneki 

*Ki zama Marar Daraja 

*Ki zama Cikin ÆŠimuwa Dan Za A Ƙureki Wataran Kiji Kunya 

*Mayaudara Na Iya Zuwa Gunki Har Su Yaudareki. 

*Ƙawaye Sunai Miki Kallon Banza. 

*Ƙin yarda Da Masoyi Komasoyiya




 

3. MUNAFURCI. Shine boyewa masoyi ko masoyiya haÆ™iÆ™anin abun dake rai, kamar kana ce mata ita kadaice budurwarka amma kuma ashe kana da wata koma wasu, idan tagane zata É—auke ka munafuki dan tasan waccar ma haka kake ce mata .  

*MUNAFURCI NASA RASHIN YARDA A TSAKANIN MASOYA, DA YAWAN FAÆŠA, DA ZARGI, KUMA KO DA KIN FADÆŠI KO KA FAÆŠI GASKIYA BAZA'A YARDA BA A WASU LOKUTAN. 

*NASA AYI BAYA-BAYA DA MASOYI KO SA SHAKKU A SOYAYYA, DA RAGE DARAJAR MASOYI. 



 

4. SON ABUN DUNIYA:
shine budurwa tana miÆ™awa saurayinta buÆ™atunta da matsallolinta na rayuwa dan yabata wani abu ko yai mata maganin su. takowacce hanya. Musali. Nunamasa afili yasai miki mota, waya babba, kayan kwalliya da sauransu. Son abunduniya nasa 

* Ayi miki kallon yar iskace koda bahakabane  

* Cikin sauÆ™i masu bata Æ´anmata na iya yaudararki da abunduniya su bataki.  

*Rashin aji da Æ™ima agun samari da rasa samari nagari. dan tsanarki za ayi. Kowa yana tsoran zuwa gunki dan dayazo za kifara yimasa tallan buÆ™atunki, sayamin kaz, yimin ankon wance, cikamin kudi nasai waya da dai sauransu  

 


 

4. ZARGI Zargi shine yawan zato ga masoyi akan abunda ba'a da tabbas. ZARGI NA BATA SOYAYYA DUKA KODA ANYI AURE. nasa ƙin Amincewa da juna da yawan fada da sauransu. Dan haka, ƴan uwa da samari ingantacciyar soyayya dolene a cire wadannan halayen marasa kyau a soyayya. abmaye gurbinsu da dabi'u masu kyau kamar su gaskiya, Ruƙon amana tausayi, haquri da juriya da sauaransu.

  ALLAH YABAMU MASOYA NAGARI

Advertisement: Buy Data Subscription at Very Chip Price  Visit:

https://www.elsub.com.ng 

Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)